/

Yan sanda sun kama yar Najeriya da Hodar Iblis a Indiya

Karatun minti 1

Sashin bincike na rundunar yan sandan Mohali da ke jihar Punjab a arewacin Indiya ta kama wata yan Najeriya da Hodar Iblis mai nauyin kilo 1.

DABO FM ta tattara cewar jami’an tsaron sun kama yar Najeriyar mai suna Faith a wani wajen lambun shakatawa a ranar Juma’a.

Rahotanni sun ce Faith mazauniyar garin Delhi ce, sai dai an lura ta na yawan zuwa garin na Mohali akai-akai.

“Mun kama ta ne sakamakon wasu bayanan sirri da mu ka samu cewa wata yar Najeriya ta na kawo wa abokan huldarta holdar iblis a wajen shakatawa da ke Phase 7”, kamar yadda wani Babban Sifirtandan yan sandan, Navjot Singh Mahal ya bayyana.

Faith ta amsa laifinta, an kuma mika ta wata yar karamar kotu in da jami’an yan sandan su ka samu sahalewar kotu domin su tsare ta a wajensu na kwana 2.

Rundunar yan sandan ta ce ta na kan binciken domin gano wadanda su ke siyan hodar iblis din a wajenta.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog