Tarihin gwagwarmayar jam’iyyar Nepu daga Muktar Mudi Spikin
Ganin karɓuwar NEPU ga talakawan duk Arewanci Najeriya, turawa da sarakunan gargajiya su ka tashi haiƙan sai sun daƙile tafiyar. Hanyoyin da su ka bi kuwa, kare ma ba zai ci ba. Domin in har aka ji wai kaima kana goyon tafiyar ba za a ƙyale ka ba. Bari na ɗan tsakuro mu ki kaɗan;
Akwai labari irin na su Aminu wanda jikan Sarkin Kano Aliyu ne. To amma kasancewarsa ɗan NEPU sai aka tura ƴan doka suka kamo shi su kai ta duka. Aka jefa shi a gadurum ya mutu.
Haka irin su Tsalha, ana ce masa Tsalha Dankasa. Shima anyi masa irin wannan. Haka aka je aka kamo shi aka yi ta jan sa a kasa aka jefa shi a gadurum na Jakara.
Ga labarin Malam Illah Ringim da aka kai shi gadurum, da niyar za a kashe shi gobe, cikin Ikon Allah masu gadin gadurum ɗin su ka tsegunta masa gobe in an zo duba shi ya yi fakare kamar ya mutu, su za su rufa masa asiri, su ce ya mutu. Haka aka yi kuwa da safe aka zo dubawa aka ce ya mutu. Wanda su ka zo dubuwar ba su yarda ba, ɗaya daga ciki ya ɗau wuta ya ɗora mai a fuska, a haka ya jure su ka yarda ya mutu, su kai umarni a fitar da shi, a haka ya sha, har ya mutu fuskarsa a ƙone take!
Ga labarin wani bawan Allah mai suna, sahabi mutumin kasar Sakkwato ne kuma dan-gani-kashe-nin jam’iyyar NEPU.
Mallam Sahabi yana daga mutanen da suka rasa rayuwarsu akan gwagwarmayar NEPU sakamakon duka da azabtarwa da aka yi masa a ranar da aka yi wani gangamin siyasa domin tarbar Sardaunan Sakkwato kuma firemiyan Jihar Arewa, Sir. Ahmadu Bello.
Lokacin da abokansa na NEPU wadanda suka hada da Binwafi da Mallam Abba Maikwaru suka je duba shi sai ya kokarta ya rubuta wasu baitocin waka ya mika musu. Ga abinda yake cewa a cikin wadannan baitocin:
1. ‘Yan uwana zan bayani,
Tun da dai kun zo gare ni.
2. Ko da dai dukkan jikina,
Ga shi duk ya samu rauni.
3. Na wuce ni babu saura,
Gobe ba damar Ku ganni.
4. San da duk dana ya girma,
Nayi roko kuyi bayani.
5. An kashe ni babu hakki,
Don kawai dan NEPU ne ni.
6. Masu shiryiwar mugunta,
Za su zo su ma su ganni.
7. Babu shakka za su zo su,
Damina ce ko da rani.
Gari yana wayewa kuwa Allah yayi mishi cikawa.
Ga wani tsakure na ganau daga hirar da Marigayi Lawan Danbazau;
“….Kamar a Katsina ana NEPU kowanne kauye. Kuma duk sanda sarakuna suka ga dama za a zo a kama mutane a daure. Har ta kai akayi doka ana kiranta yin sallah da niyyar NEPU; noma da niyyar NEPU; taron suna ko daurin aure da niyyar NEPU; hira da niyyar NEPU. Wannan ya nuna duk sadda aka ga dama za a zo a kama ka.
‘Kamar yanzu idan aka zo aka tarar da mu muna hira a nan cikin dakina, to sai dagaci yaje ya gaya wa hakimi; hakimi sai ya turo ‘yandoka ko ‘yansanda su zo duk su kama mu. Sai kuma a kai mu gaban alkali a ce an zo an tarar muna hira da niyyar NEPU; wai hirar da muke yi wayon yin NEPU ne. Idan kuma aka zo aka tarar da iyali sun taru suna noma idan aka ga dama za a iya kama su ace nomar da suke da niyyar NEPU suke yi.
‘Kama mutanen ya wuce misali. Mutane da yawa an daure su. Wanda aka daure shekara guda sai yayi wata takwas sannan alkalin kotun sama yace ya sake shi ya tafi shikenan. Dama bai yi wani laifi ba. Idan kuma wata shida aka daure mutum, sai kati wata biyar sannan alkali yace zai ji apil dinka.
‘Haka akayi da gardaye masu karatun kur’ani a Borno, domin kusan duk gardayen Nijeriya ‘yan NEPU ne. Don haka za a zo a tad da abinda ake kira tsangaya – wato wurin zaman karatun babban malami – a sa wuta, a babbake wannan tsangayar; a kona allunan har da kur’ani. A daure na daurewa wasu kuma a murde a haka rami cikin rairayi a binne su. Sai kana tafiya kan titi daga gefe rana in ta dafa su hakanan sai ka ji ‘PAL’ , gawa tayi bom, ‘tan hanji da hanta da sauransu sun fito. Haka akayi tayi a Borno, akai ta kashe mutane saboda wai basu yi NPC ba.
‘A Sakkwato ma dai-dai da wannan aka rika yi. A Sakkwato duk masu darikar Tijjaniyya kusan duk baki dayansu ‘yan NEPU ne. Wannan ya jawo musu muguwar wahala. Akwai sanda aka kamo mutane gari-gari sun fi dari aka zo aka zuba su cikin sito na auduga wanda babu taga, an an suke kwana.